Kungiyar Tarayyar Turai (EU) na wani yunkuri na maye gurbin gas din da take saya daga kasar Rasha, da na Najeriya sakamakon yakin da Rasha take yi a Ukraine, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.
A wata ziyara da ya kai Najeriya mataimakin babban daraktan hukumar gudanarwa ta Tarayyar Turai Matthew Balwdin ya ce, ya ziyarci Najeriya ne domin tattaunawa da jami’an kasar don kulla yarjejeniyar.
A halin da ake ciki dai, tarayyar turai na samun kashi 14 cikin 100, na gas din da take amfani da shi daga Najeriya.
Shugabannin kasashen Turai sun sanya wa Rasha tarin takunkumai saboda mamayar da ta yi wa Ukraine.
Kungiyar ta EU dai na son rage yawan gas din da take shigarwa daga Rasha da kashi biyu cikin uku.