Kungiyar Masu Kafafan Yaɗa Labarai ta Arewa (NBMOA), ta shawarci Gwamnatin Tarayya da ta mika hannun abokantaka ga manema labarai.
Hukumar Yada Labarai ta Kasa (NBC) ta ci tarar Trust TV tarar Naira miliyan 5, saboda shirinta na “Nigeria’s Banditry: The Inside Story”.
An kuma ci tarar Multichoice Nigeria Limited (DSTV masu mallakin NTA-Startimes Limited, da Telcom Satellite Limited (TSTV) tarar Naira miliyan 5 kowannensu, saboda yaɗa labarai na BBC na “The Bandit Warlords of Zamfara”.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, mukaddashin shugaban NBMOA, Abdullahi Yelwa ya jaddada cewa, tara ba zai kawo karshen rashin tsaro a Najeriya ba.
Kungiyar ta bukaci hukumar ta NBC da ta yi watsi da matakin da kuma samar da hadin kai tsakanin kafafen yada labarai da gwamnati