Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya lashe kujerar sanatan Sokoto ta Kudu, a zaɓen cike gibi da ya gudana a jiya da ƙuri’a 4,976.
Tambuwal wanda ya yi takara ƙarƙashin jam’iyyar PDP ya kayar da sanata mai ci ne, na jam’iyyar APC Ibrahim Ɗanbaba Dambuwa.
A bayanin da baturen zaɓen Farfesa Abubakar Bagudo ya yi, ya ce Aminu Waziri Tambuwal ya samu ƙuri’a 100,860 yayin da abokin karawarsa Danbaba ya samu 95,884.
Tambuwal shi ne gwamna na uku da ya samu nasarar ɗarewa kujerar sanata cikin gwamnoni 10 da suka nemi kujerar a Najeriya.


