fidelitybank

Tambuwal ya bayar da Naira miliyan 30 ga iyalan da ‘yan bindiga suka kashe a Kebbi

Date:

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya bayar da tallafin Naira miliyan 30 ga iyalan wadanda harin ‘yan bindiga ya rutsa da su a jihar Kebbi.

A ranar Litinin ne ‘yan banga suka yi wa Yan-Sa-Kai kwanton bauna, inda suka kashe 65 daga cikinsu, yayin da a ranar Talata, ‘yan bindigar suka kashe wasu sojoji a jihar.

Tambuwal, ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar jaje ga takwaransa gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, bisa rasuwar jami’an Yan-Sa-Kai, da kuma jami’an soji da aka kashe a masarautar Zuru.

Gwamnan jihar Sokoto ya bukaci al’ummar jihar da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai, domin kara kaimi ga kokarin gwamnatin tarayya da na jihohi wajen yakar wannan barazana.

A nasa martanin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya ce, jihohin Kebbi da Sokoto, iyali daya ne babba. Ya ce, “Mu iyali daya ne, duk abin da ya shafi daya ya shafi kowa.” a cewar rahoton Daily Trust.

benue news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp