Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, ya bayyana alhininsa kan rasuwar daya daga cikin kwamishinonin sa, Usman Suleiman.
Jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party, wanda ke kula da ma’aikatar harkokin addini, ya rasu ranar Juma’a bayan rashin lafiya.
Tambuwal ya bayyana shi a matsayin musulmi mai kishin addini kuma jajirtaccen jami’i wanda ya yi aiki da kyau a dukkan ma’aikatun da ya jagoranta.
Karanta Wannan: Ina murna da aka kayar da Tambuwal – Fayose
Gwamnan ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar musamman iyalai da makusanta Suleiman.
Tambuwal ya ci gaba da yi masa addu’ar samun lafiya, kuma ya roki Allah Madaukakin Sarki da Ya ba shi Aljannah firdaus ta zama makoma ta karshe.
An yi jana’izar mai rike da sarautar Danmadamin Isa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Wadanda suka halarci jana’izarsa sun hada da Mataimakin Gwamna Mannir Dan’iya da Sakataren Gwamnati Mainasara Ahmad da Shugaban Ma’aikata Abubakar Dan-Shehu da Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Bello Goronyo da dai sauransu.