fidelitybank

Tallafin Mai: Ana biyan sama da biliyan 400 duk wata – NNPCL

Date:

Kamfanin mai na NNPCL na kasa ya ce, adadin kuɗin da ake biya a matsayin tallafin man fetur a kowanne wata ya haura naira biliyan 400.

Kamfanin dillancin labaran NAN ya ruwaito shugaban kamfanin Mele Kyari, na bayyana haka a Abuja babban birnin ƙasar a lokacin kammala sauya wa kamfanin fuska..

Kyari ya ƙara da cewa kamfanin na NNPCL na kashe kusan naira 202 a matsayin tallafi ga kowacce litar mai a faɗin ƙasar

Ya kuma ce a kowacce rana kamfanin na samar da litar mai miliyan 65 domin wadata ƙasar da man fetur.

Shugaban kamfanin ya ce kamfanin zai ci gaba da yin abin da ya wajaba a kansa na samar wa ‘yan ƙasar man da suke buƙata.

Yana mai cewa biyan sama da naira biliyan 400 a kowane wata a matsayin tallafin man na matuƙar yin tarnaƙi ga harkokin kuɗin kamfanin.

Ya ci gaba da cewa, kamfanin na NNPCL shi ne kaɗai kamfanin da ke shigar da mai cikin ƙasar, kuma zai ci gaba da taka rawa cikin shekaru masu zuwa duk da yawan kuɗin tallafin da yake biya.

Mele Kyari ya ce ‘yan kasuwa masu zaman kansu sun daina shigar da mai cikin ƙasar sakamakon wahalar da suke fuskanta wajen samun Dalar Amurka da ake buƙata domin shigar da man zuwa ƙasar.

latest news nnn

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp