Kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ke biya a matsayin tallafin lantarki ya ƙaru zuwa naira biliyan 199.64 a watan Disamban 2024, kamar yadda alƙaluma daga hukumar kula da lantarki NERC suka nuna.
Tashar Channels ta ruwaito daga wani rahoto da hukumar ta fitar cewa kuɗin tallafin ya ƙaru da kashi 2.76 wato naira biliyan 199.64 a wannan watan na Disamban, daga naira biliyan 194.26 a watan Nuwamban bana.
Hukumar NERC ta ce an samu ƙarin ne saboda faɗuwar darajar naira, kasancewar an ƙiyasta darajar dala ne a naira 1,687.45 a kasafin kuɗin kasar, da hauhawar farashin kayayyaki da ya ƙaru zuwa kashi 33.9.
Rahoton ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya ba ta canja farashin lantarki ba a ɗan tsakankanin.