Taliban ta ce za a soke duk wata dokar da ba ta musulunci ba a Afghanistan .
Taliban ta ce za a dawo tsantsar tsarin Shari’ar musulunci a ƙasar.
Shugaban ƙungiyar Hibatullah Akhundzada ya ce sun shirya hulda da ƙasashen duniya irin yadda shari’ar musulunci ta buƙata.
Tun bayan da Taliban ta dawo kan mulki a 2021, ƙugiyar ta ƙi amince wa ɗalibai mata komawa makarantun sakandare, batun da ya jawo Allah-wadai a faɗin duniya.