Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana damuwa kan sabuwar dokar Taliban da ta tilasta wa mata rufe fuska a Afghanistan.
“Na kaɗu da da sanarwar da Taliban ta fitar na cewa dole ne mata su rufe fuskokinsu a bainar jama’a kuma lalura kawai za ta fitar da su daga gida,” kamar yadda ya wallafa a Twitter.
Guterres ya yi kira ga Taliban su cika alƙawalin da suka ɗauka ga matan Afghanistan da kuma haƙƙin da ya rataya a wuyansu ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa na kare haƙƙin ɗan adam.