‘Yan kungiyar Taliban da masu goyon bayansu na kai komo a babbar hanyar da ke kudancin birnin Kandahar, wato cibiyar ‘yan kungyar.
Mayaka dauke da makamai, a kan ababen hawa na daga tuta mai launin fari da baki a yayin da yara kananan kuma cike da murna ke zaune a gefensu.
Ga ‘yan kungiyar ta Taliban, yau ce ranar bikin samun ‘yanci daga dakarun kawancen da Amurka ke jagoranta. A cewar BBC.
Da yawa daga cikin ‘yan kasar ta Afghanistan ba su san makomar kasar ba har yanzu kamar yadda ake ci gaba da rufe makarantun ‘yan mata a kasar.
Ba ko ina ne ake zaman kunci a kasar ba, alal misali a yankunan karkara, musamman wadanda ke a kudanci da gabashin kasar, wadanda a baya aka yi taho mu gama sosai, a yanzu mazauna kauyukan na zaman lafiya ba tare da wata fargaba ba.
Abin da yake hada kan kasar shi ne yadda ake nuna damuwa a game da matsalar tattalin Arziki da mawuyacin halin da ‘yan kasar ke ciki, ga talauci da kuma karuwar rashin abincin mai gina jiki saboda dakatar da bayar da kudaden waje.


