Hukumar yada labarai ta Taliban ta zane mutum 12 a garin Firoz Koh, babban birnin Lardin Ghor.
Shugaban yada labarai na Taliban Sakhir Rahman Fayez, kuma shugaban kotun daukaka kara na lardin ya ce, “kotun nan ta tuhumi mutum 12 ciki har da mace da aikata abin da bai dace ba, rashin da’a, sata, da kuma wadanda suka sha kayan maye, duka an zane su a filin wasan kwallon kafa na garin.
Ya ce “an zargi mutum 6 daga cikinsu da yin sata, wasu 4 kuma daga cikinsu an zarge su da shan giya, an zargi mutum daya kuma da yin rashin da’a, mutum daya kuma an zarge shi da guduwa daga gida, kuma duka na zane su.”
A watan jiya, Taliban ta zane maza da mata a bainar jama’a, kuma shi ne hukuncin farko da aka yi a bainar jama’a a Farah.