fidelitybank

Talauci da rashin tsaro na iya barazana ga zaɓen 2027 – Rahoto

Date:

Ƙungiyar fafutikar kare haƙƙin ɗan’adam da tabbatar da dimokuraɗiyya ta YIAGA Africa ta ce babban zaɓen Najeriya na shekarar 2027 na fuskantar barazana saboda ƙaruwar talauci da rashin tsaro a ƙasar.

YIAGA ta bayyana haka ne a Abuja a lokacin da take gabatar da rahoton bincikenta, inda daraktan ƙungiyar, Samson Itodo ya ce talaucin da ya wa ƴanƙasar katutu zai iya jawo ƙaruwar sayen ƙuri’a a zaɓen, musamman ta hanyar amfani da abinci domin sayen ƙuri’a.

Ya ce, “wannan zaɓen akwai alamar a yi amfani da kuɗi sama da zaɓukan baya. Yanayin talauci da yunwar da ƴanƙasar ke ciki zai sa a samu sauƙin sauya tunanin masu zaɓe,” in ji shi, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Rahoton ya ƙara da cewa maimakon matsin tattalin arzikin da ƙasar ke ciki ya sa mutane su fusata su fito zaɓe, “akasin hakan za a iya samu, domin ƴansiyasa za su yi amfani da hakan domin sauya musu tunani da kuɗi.”

Rahoton ya kuma bayyana cewa ana samun ƙaruwar ƴanƙasar da suke dawowa rakiyar Hukumar INEC, wanda ƙungiyar ta ce ya ƙaru bayan zaɓukan gwamnonin jihohin Kogi da Edo.

nnnnews

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ganduje ba dan cin hanci ba ne – Martanin Garba Ga Gwamnatin Kano

Tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba,...

Kungiyar Malaman Jami’o’i bangaren BUK sun yi zanga-zangar Lumana

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Bayero Kano (BUK),...

An gargadi Borno da Yobe da Jigawa su zama cikin shirin ambaliya

Akwai yiwuwar samun ambaliya a jihohin Borno, Jigawa da...

Kano na cikin jihohin da ba su yi katin zabe sosai ba – INEC

Bayanan da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya...

Mun gano filin wasa na Sani Abacha ba shi da inganci – NPFL

Hukumar shirya gasar cin kofin kwararru ta kasa (NPFL),...

Jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna ya ya fadi

Jirgin ƙasa ɗauke da fasinjoji da ya taso daga...

Jami’in mu bai saci naira biliyan 6.5 ba – Gwamnatin Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta karyata rahoton da ya zargi...

Gwamnatin Kano ta gargadi Matasa da ‘yan Gwangwan kan sayen kayan gwamnati

Gwamnatin Jihar Kano ta gargadi matasa da ’yan kasuwa...

NIMET ta gargai Borno kan ambaliya da sauran jihohi

A baya-bayan nan ne hukumar hasashen yanayi ta Najeriya...

An kashe kwamandan Boko Haram a tafkin Chadi

Sojojin Jamhuriyar Nijar sun sanar da kisan wani jagoran...

Hisbah za ta yi wa ‘yan Daban Kano aure

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta sanar da wani...
X whatsapp