Sanata Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa ya ce, talauci bai san bambancin addini ko ƙabila ba.
Ndume ya bayyana haka ne a shafinsa na X bayan ya wallafa wani faifan bidiyo da BBC ba ta tantance ba, na yadda mutane suka yi wani dogon layin amsar tallafi a ƙofar gidan Shugaban Ƙasa Bola Tinubu na Legas a ranar Kirsimeti.
A bidiyon akwai mata masu sanye da hijabi da marasa shi, da maza masu dogayen kaya da masu ƙanana duk a layin.
Ndume ya ce, “layin karɓar tallafi a gidan Shugan Ƙasa Tinubu da ke Legas yana koyar da wani darasi: Talauci ba shi da ƙabila da addni da siyasa. Matsala ce da take buƙatar haɗin kai domin samun gyara na bai-ɗaya.”
Ana dai kallon kalaman na Ndume tamkar shaguɓe ga shugaban ƙasar domin nuna yadda ƙasar ke fama da talauci.