Kafar yaɗa labarun Al Jazeera ta maka sojojin Isra’ila a kotun hukunta manyan laifuka ta ICC game da kisan ɗaya daga cikin ma’aikatanta, Shireen Abu Akleh.
Lauyan Al Jazeera ya ce wannan muhimmiyar rana ce saboda sun gabatar da cikakkun shaidu a madadin kafar yaɗa labaran kuma abin da Al Jazeera ke nema shi ne a gaggauta sauraron ƙarar ba tare da ɓata lokaci ba.
An harbe ƴarjaridar ne tana tsaka da aiki yayin wani samamen sojojin Isra’ila a yankin Gabar Yamma da Kogin Jordan cikin watan Mayu.
Rundunar sojin Isra’ila ta tabbatar cewa akwai yiwuwar sojojinta ne suka halaka Ms Abu Akleh amma a cewarsu bisa kuskure.
Firaminista Yair Lapid ya yi watsi da batun gudanar da bincike daga waje.
Al Jazeera ta ce shaidun da za ta gabatar ga kotun ta ICC za su haɗa da bidiyon da ke nuna lokacin da sojojin Isra’ila suka harbi ƴar jaridar. In ji BBC.