Mambobin majalisar dokokin kasar nan sun samu rarrabuwar kawuna, dangane da fitowar ‘yan takarar shugabancin jam’iyyar APC na kasa har su uku daga majalisar tarayya.
Jam’iyyar APC ta ce, za ta zabi sabon kwamitin ayyuka na kasa karkashin jagorancin shugaban a babban taronta na kasa da aka shirya yi a ranar Asabar.
‘Yan takarar uku wadanda dukkansu ‘yan majalisar dattawa ne, Abdullahi Adamu, Sani Musa da Tanko Al-Makura.
Sanatocin dai wadanda dukkaninsu sun fito ne daga shiyyar Arewa ta tsakiya, sun fafata ne da wasu masu neman tsayawa jam’iyya mai mulki, wadanda ba ‘yan majalisar tarayya ba.
A makon da ya gabata ne Adamu da Al-Makura suka gana da jiga-jigan jam’iyyar APC a majalisar wakilai, inda daga bisani suka ba wa ‘yan majalisar tikitin tsayawa takara, idan ya zama shugaban jam’iyyar. Har yanzu Musa bai gana da kwamitin ba.
Al-Makura da Adamu tsoffin gwamnonin jihar Nasarawa ne.bYayin da Al-Makura ke wakiltar mazabar Nasarawa ta tsakiya, Adamu yana wakiltar mazabar Nasarawa ta Yamma a majalisar dattawa.