fidelitybank

Takarar Sha’aban Sharada ta wasa ce – Rarara

Date:

Shahararren mawakin nan Dauda Kahutu Rarara, ya ce, ba da gaske Sha’aban Ibrahim Sharada ya ke takarar gwamna ba, shi ya ajiye tafiyar sa ya koma wajen Gawuna.

Rarara ya ce, duk da shi ne ya tsayar da Sha’aban Ibrahim Sharaɗa takarar Gwamna, amma daga bisani ya gano ta wasa ce.

Rarara ya bayyana hakan ne a hira da Jaridar Intanet ta DCL Hausa suka yi da shi, inda ya zargi Sha’aban da shinshinar PDP a zaɓen Shugaban ƙasa da ya gabata maimakon APC da suka yi yarjejeniya.

Karanta Wannan: Zan inganta masana’antu da gayyato masu zuba jari a Kano – Sha’aban

” Ni na tsayar da Sha’aban takarar gwamnan da yake yi, ya zo ya same ni yace yana so yayi takarar gwamnan Kano kuma gashi duk jam’iyyun sun tsayar da yan takara, ni da wasu mutane da ba sai na fadi sunansu mu muka je muka Nemo masa jam’iyyar ADP domin yayi takara a cikin ta, don haka duk wata maganar takarar Sha’aban ni nasan ta Kuma na bar shi ne saboda na fahimci ba takarar gaske yake ba”. Inji Rarara

” A cikin Mutane dubu daya da suke tare da Sha’aban dari bakwai ni na kawo su ko kuma wadanda na kawo su suka kawo su, don haka ni na tsayar da shi takarar Kuma na bar shi ne saboda na fahimci ba takarar gaske yake ba “.

A cikin hirar Rarara ya bayyana cewa Nasiru Gawuna yafi kowanne dan takarar gwamnan kano cancanta Saboda nagartar da yake da ita da Kuma yadda ya mika lamarin takarar sa ga Allah.

vanguard (nigeria)

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp