Mutumin da ke takarar sanata karkashin inuwar jam’iyyar APC a Yobe ta Arewa a Najeriya, Bashir Sharrif Machina, ya ce ba zai sauka ko ya janyewa kowa takararsa ta majalisar dattawa ba.
Wadannan kalamai na Bashir Machina na zuwa ne a daidai lokacin da take ƙasa take dabo game da makomar siyasar shugaban majalisar dattawa ta ƙasa, Ahmed Lawan, bayan ya rasa takarar shugaban ƙasa a APC da ya nema.
Tun bayan kammala zaben fitar da gwani shugaban kasa a APC dambarwa ta kunno kai kan yiwuwar rasa takararsa ta sanata bayan ya shafe fiye da shekara ashirin yana wakiltar al’ummarsa a Majalisun Tarayyar ƙasar.
Rahotanni a baya-bayan nan sun yi ta yaɗa cewa Sanata Ahmad Lawan ya samu takarar ɗan majalisar da yake kai yanzu, sai dai mutumin da ya ci takarar tun da farko, Bashir Sharif Machina ya ce har yanzu shi ne ɗan takarar Sanatan Yobe ta arewa a APC.


