fidelitybank

Takarar Al-Mustapha da ƴan jam’iyyar AA ta shiga tsilla-tsilla

Date:

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta yi watsi da sunayen ‘yan takarar jam’iyyar Action Alliance (AA), ciki har da sunan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Manjo Hamza Al-Mustapha mai ritaya.

Sai dai wannan umarni da aka bai wa ‘yan jarida a Kaduna a ranar Asabar din da ta gabata, ya umurci hukumar zaben ta nuna jerin sunayen ‘yan takarar da shugabancin jam’iyyar a karkashin Adekunle Rufai Omoaje ya mika mata.

Hukumar zaben ta hanyar kin amincewa da jerin sunayen ‘yan takarar da bangaren Omoaje ya gabatar mata, a cewar kotun da ke karkashin Mai shari’a Z.B. Abubakar.

Mai shari’a Abubakar wanda ya bayar da misali da sashe na 29 (1) na dokar zabe, 2022, ya umurci INEC da ta gaggauta buga sunaye da adireshi na dukkan ‘yan takarar da Omoaje ya mika a madadin kungiyar Action Alliance.

“Ta hanyar tanadin sashe na 29 (1) na dokar zabe, 2022, ya kamata INEC ta buga ta hanyar nunawa a ofishin da ya dace na INEC da kuma a shafinta na intanet.”

A cewar hukuncin kotun, akwai yiwuwar jerin sunayen ‘yan takarar da Omoaje ya bayar zai maye gurbin ‘yan takarar INEC da aka riga aka bayyana, ciki har da dan takarar shugaban kasa, Manjo Hamza Al-Mustapha mai ritaya.

nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Kashe jagoran Iran Ayatullah shi ne kawo ƙarshen rikici – Isra’ila

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce duk wani shiri...

Jerin sunayen masu Fashin Waya 51 da aka kama a Kano

Rundunar ƴansandan Kano, ta fitar da jerin sunayen Mutane...

Iran ta dakatar da tashin jirgi a ƙasarta

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Iran ta...

Poland za ta kwashe dukkannin ƴan ƙasarta daga Isra’ila

Poland na shirin kwashe kusan ‘yan kasarta 200 daga...

Kisan Binuwai abun haushi ne bai kamata a ƙyale ba – Atiku

Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da Kisan Benue, tare...

Ƴan Bindiga sun ajiye makamai a Katsina

Wasu fitattun jagororin ƴanbindiga da suka addabi yankunan ƙaramar...

Iran ta rataye Mutumin da ya yi mata leƙen asiri

Iran ta ce ta aiwatar da hukuncin kisa ga...

Isra’ila ta ci gaba da neman Mutanen da suka maƙale

Tawagar masu aikin ceto a Isra'ila na ci gaba...

Kotu ta bayar da umarni a kashe Matashi ɗan shekara 23 a Kano

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 23 ƙarƙashin mai...

Iran ta na ci gaba da luguden makami a kan Isra’ila

Iran ta ci gaba da lugudan wuta a Isra'ila...

An yi sulhu da shugabannin ƴan Bindiga a Katsina

Wasu al'ummar Katsina, sun yi sulhu da wasu shugabannin...

Za a fuskanci ambaliya a wasu jihohin – NIMET

Hukumar kula da yanayi ta NiMet, ta ce akwai...
X whatsapp