fidelitybank

Takarar 2023: Kwamishinoni 53 da hadiman gwamnoni sun ajiye aikin su

Date:

Rahotanni daga jihohi da dama a fadin tarayyar kasar nan sun nuna cewa, akalla Kwamishinoni 53, da ma’aikatan gwamnoni da dama ne suka ajiye aikinsu domin tsayawa takara a zaben 2023.

Hakan ya faru ne bayan wasu gwamnoni sun bukac e su sauka daga mukamansu domin yin biyayya da sashe na 84(12) na dokokin zabe da ya umarci masu sha’awar su yi murabus.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ministocin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da ake ganin suna son tsayawa takara, suke ci gaba da zama a kan mukamansu.

Cikinsu akwai Ministan Sufurin Najeriya, Rotimi Amaechi, Ministan Kwadago, Sanata Chris Ngige; da Ministan Shari’a Abubakar Malami, da sauran masu rike da manyan mukamai a hukumomin gwamnati da suka fara hararo wasu daga cikin kujerun siyasa da suka hada da ta shugaban kasa, da gwamnoni da ‘yan majalisu da sauran.

Rahotanni sun nuna cewa Kwamishinoni da masu ba da shawara akalla 12 ne suka mika wa Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na Jihar Kwara takardun murabus.

A jihar Kano, bayanai sun nuna cewa akalla Kwamishinoni 10 ne suka ajiye aiki cikinsu har da Mataimakin Gwamna Nasir Gawuna, wanda shi ne Kwamishinan Noma.

A Delta, rahotanni sun ce shugaban ma’aikatan gwamnan jihar Ovie Agas,da Kwamishinoni tara sun sauka daga kujerunsu domin tsayawa takarar a zaben 2023.

vgn news today 2021

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp