Wata akanta ƴar shekara 47, mai suna Afolake Abiola, ta kashe kanta ta hanyar shan maganin kashe kwari.
Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 27 ga Mayu, 2022, a gidanta mai lamba 1 Abayomi Kukomi Close a Osapa London, Lekki, Legas.
Jaridar Vanguard rawaito cewa, Afolake wadda ba ta yi aure ba, kuma ba ta taɓa haihuwa ba, ta na fama da bakin ciki na wani dan lokaci kafin ta kashe ta.
In ji wani danginsu, wanda aka sakaye sunansa ya ce, “ta jima tana fama da baƙin ciki saboda babu miji da ɗa.”
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya ce, lamarin ya faru ne a ranar 27 ga watan Mayun 2022.
Ya ce: “Lokacin da ‘yan sandan suka isa wurin, ‘yan uwanta suna wurin, kuma a hukumance sun bukaci a sako gawar domin su samu damar binne ta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
A bisa dalilan jin kai an sako gawarta ga iyalanta domin a binne ta.”