Rundunar ƴan sanda a jihar Akwa Ibom, sun ce ƴan bindiga sun yi garkuwa da mai shari’a ta wata babbar kotu tare da kashe jami’in da ke ba ta tsaro.
Bayanai na cewa an yi garkuwa da Mai shari’a Joy Uwanna a hanyarta ta komawa gida bayan ta tashi daga aiki a kotun da ke kan titin Uyo zuwa Okoboin a garin Oron.
Ana zargin ƴan bindigar sun buɗe wuta tare da harbin ɗan sandan da ke tare da mai shari’ar kafin daga bisani su yi awon gaba da ita da kuma direbanta.
Kakakin ƴan sandan jihar, Odiko Macdom ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici inda ya ƙara da cewa jami’an tsaro suna bincike a kai.
Zuwa yanzu babu wanda ya ɗauki nauyin kai harin amma garkuwa da mutane domin kuɗin fansa da ƴan bindiga ke yi abu ne da ya zama ruwan dare a wasu sassan Najeriya.


