Shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayyana tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari da “ɗan kishin ƙasa, soja, kuma dattijon ƙasa wanda ba za a taɓa mantawa da sadaukarwar da ya yi ba”.
Cikin wata sanarwa a yau Lahadi, Tinubu ya ce ya “kaɗu sosai da jin labarin mutuwar”, yana mai cewa “hidimar ƙasa, da alfarma, da sadaukar da kai ga haɗin kai da cigaban ƙasa” ne za a ci gaba da tunawa da tsohon shugaban da su.
Buhari ya rasu a yau Lahadi a wani asibiti da ke birnin Landan yana da shekara 82. Fadar shugaban ƙasa ta ce ya rasu ne bayan fama da doguwar jinya.
Nan gaba Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima zai je Landan ɗin domin yi wa gawar Buhari rakiya zuwa Najeriya, inda za a yi jana’izarsa.
Shugaba Tinubu ya jagoranci taron majalisar zartarwa na gaggawa a yau Lahadi domin girmama marigayin.