fidelitybank

Tabbas an samu bullar cutar Anthrax a Najeriya – Gwamnati

Date:

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da ɓullar cutar anthrax a hukumance.

Wata sanarwa da ma’aikatar noma da raya karkara ta ce an kai rahoton dabbobin da ke nuna alamun yiwuwar kamuwa da cutar anthrax a wata gona da ke Suleja a Jihar Neja zuwa ofishin babban jami’in kula da dabbobi na Najeriya a ranar 14 ga watan Yuli.

Jaridar daily trust ta ruwaito cewa ma’aikatar ta ce lamarin ya faru ne a wata gonar dabbobi da ta ƙunshi shanu da tumaki da awaki da ke Gajiri a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a ƙaramar hukumar Suleja a jihar Neja, inda wasu daga cikin dabbobin ke da alamomi da suka haɗa da zubar jini daga sassan jikinsu, hanci, idanu da kunnuwa.

Ta ce tawagar masu bayar da agajin gaggawa da ta haɗa da ƙwararrun ma’aikatan lafiya na tarayya da na jihar sun ziyarci gonar don gudanar da bincike na farko tare da tattara samfurori daga dabbobin da suka kamu da cutar.

Ma’aikatar ta ce gwaje-gwaje na Cibiyar Nazarin Dabbobi ta ƙasa ta tabbatar da kamuwa da cutar, “wanda ke nuna alamar cutar anthrax ta farko a Najeriya a cikin ‘yan shekarun nan”.

Ta yi nuni da cewa, gwamnatin tarayya ta yi gargaɗi ga ‘yan Najeriya makonnin da suka gabata bayan samun labarin ɓarkewar cutar anthrax a Arewacin Ghana inda duk dabbobin da suka kamu da cutar suka mutu.

Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnati ta yi kira ga ƴan Najeriya da su gaggauta kai rahoton bullar dabbobin da ke zubar da jini a jikinsu ga hukumomin kiwon lafiyar dabbobi ko kuma ma’aikatan aikin gona.

thisdaynews

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp