Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ta tabbatar da kashe jami’an ‘yan sanda uku da ke aikin rakiya a Fatakwal a ranar Alhamis.
Lamarin ya faru ne a gadar sama ta Rumuokoro da misalin karfe 3 na rana inda ‘yan bindigar suka yi awon gaba da wadanda abin ya shafa tare da kwashe wasu makudan kudade da ba a bayyana adadinsu ba.
A cewar shaidun gani da ido, maharan sanye da kakin soji sun yi ta yawo a kusa da mahadar yayin da suke jiran harin da aka kai musu.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Ribas, SP, Grace Iringe-Koko, wadda ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce ‘yan sandan na ci gaba da tattara bayanai domin sanin halin da ake ciki a harin.
Ta bayyana wanda aka yi garkuwa da shi wani jami’in kula da mai ne.