Gwamnatin tarayya ta jaddada kudirinta na magance matsalolin rashin tsaro da suka addabi sassan kasar nan.
Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun ne ya bayar da wannan tabbacin yayin da ya jagoranci tawagar shugaban kasa zuwa jihar Yobe domin jajantawa gwamnati da al’ummar jihar kan lamarin da ya faru a garin Mafa.
Ya ce ziyarar ta nuna aniyar gwamnatin tarayya na kawo karshen rashin tsaro da samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin kasar nan.
A madadin shugaba Tinubu, Ministan ya jajantawa iyalan wadanda harin Mafa ya rutsa da su da al’ummar jihar Yobe.
Shi ma mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu, wanda shi ma a tawagar ya tabbatar da cewa kawo karshen ta’addanci da ‘yan fashi a Najeriya na kara kusantowa.
Ya yabawa sojoji da sauran kungiyoyin tsaro bisa kokarin da suke yi na dakile ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas da sauran laifuka a fadin kasar nan.
“Hukumomin tsaro sun yi matukar ban al’ajabi, inda suka yi sadaukarwa don kare rayuka da dukiyoyi a kasar nan.
“Abin da muke gani yanzu shine farkon ƙarshe, lokaci ne kawai, za a tabbatar da tsaron ƙasar gaba ɗaya”, in ji NSA.
Gwamna Buni ya bayyana jin dadinsa da ziyarar, yana mai cewa, “gwamnati da al’ummar jihar Yobe sun samu fahimtar juna a wannan ziyarar”.
Ya yaba wa Shugaba Tinubu “saboda samar da shugabanci ga kasa a cikin mawuyacin hali”.
Hakazalika, kwamitin ayyuka na kasa (NWC) na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, sun je Damaturu domin jajantawa gwamnati da jama’a.
Ganduje ya ce hukumar ta NWC ta je jihar ne domin ta gane da gwamnati da al’ummar jihar a wannan lokaci na kai hare-haren wuce gona da iri da kuma kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
“Muna cikin dangin Yobe, muna jin zafi da bakin ciki da gwamnati da al’ummar jihar Yobe suka sha, kuma muna nan don jajantawa ‘yan uwanmu kan wannan mummunan lamari,” in ji Ganduje.