Rahotanni sun bayyana cewa, wasu ‘yan ta’adda sun kashe wasu ‘yan kauye hudu a karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.
A cewar wani mazaunin unguwar, Mista Didan Auta, daya daga cikin wadanda abin ya shafa shi ne sabon malamin makarantar firamare da aka dauka aiki mai suna Elisha Arziki.
A cewarsa, an kai harin ne a yankin Gefe da Tudun Mare duk a karamar hukumar Kajuru.
“’Yan bindigar sun kashe shugaban matasan tare da mutanen kauyen biyu a lokacin da suka kai farmaki kauyen ranar Lahadi. An yi jana’izar su a ranar Litinin,” inji shi, inda ya ce an kashe malamin ne a daren Lahadi a Tudun mare.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, bai amsa kiransa na tabbatar da hakan ba har ya zuwa lokacin da ake cike wannan rahoto.