fidelitybank

Ta’adda: An sace ɗan takarar gwamna a Filato

Date:

Rahotanni daga jihar Filato na nuni da cewa ƴan bindiga sun sace tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar Filato a zaɓen 2019, Nkemi Nicholas Nashe.

Jaridar Punch ta rawaito cewa, wani makusancin Mista Nshe na cewa, jama’ na zaman fargaba tun bayan faruwar wannan lamari a Shendam.

Mista Nashe wanda jigo ne a Jam’iyyar PDP, ya taɓa riƙe muƙamin Shugaban Ƙaramar Hukumar Shendam a baya.

Shi kansa gwamnan jihar mai ci a yanzu Simon Lalong ya fito ne daga Ƙaramar Hukumar Shendam.

Sace Mista Nshe na zuwa ne ƙwanaki kaɗan, tun bayan sakin wani basarake a jihar ta Filato da a ka sace, Charles Mato Dakat.

Sai dai sojoji da ke jihar sun bayyana cewa sun kama mutum takwas da su ke zargi da hannu a sace basaraken. Kamar yadda BBC ta rawaito.

tribune news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...

Alhazai Miliyan Ɗaya da Rabi ke tsayuwar Arfa

Dubun dubatar alhazai daga sassan duniya na hawan Arafa...

Sarkin Kano na 15 ya dakatar da yin hawan Sallah

Mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado...

Maniyacin jihar Kano da yake kokarin zama Alhaji ya rasu a Saudiyya

Daya daga cikin alhazan jihar Kano, Shu’aibu Jibrin, an...

Tinubu ya bayar da tallafin Biliyan Biyu da Tirela 20 na Shinkafa ga al’ummar Mokwa

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce, shugaban ƙasar...

Gwamna Adeleke na Osun ya gana da Tinubu

Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya kai ziyara ga...

An samu gawar mutane 7 a ambaliyar Neja

Rahotonni na cewa masu aikin ceto sun zaƙulo gawar...
X whatsapp