fidelitybank

Ta hanyar da ta dace shugaban Binance ya fice daga Najeriya – Makusancinsa

Date:

Amurka ta ce tana da masaniya a kan rahotannin tsare ɗanƙasarta a Abuja.

A watan da ya gabata ne aka kama shugaban kamfanin Binance, Tigran Gambaryan tare da abokin aikinsa, Nadeem Anjarwalla, wanda ke da fasfon Birtaniya da Kenya a wani ɓangare na binciken kaucewa biyan haraji da gwamnatin Najeriya ke yi wa kamfanin na kuɗin kirifto.

Mai magana da yawun ofishin jakadancin Amurka a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa, “A duk lokacin da aka samu wata matsala ta tsare ɗanƙasarsu a wata ƙasa, to ofishin jakadancin da ke ƙasar na yin duk mai yiwuwa wajen bayar da taimakon da ya dace.”

Ofishin jakadancin ya ƙi bayar da cikakken bayanai game da tsare ɗanƙasar, yana mai cewa saboda dalilai na sirri.

Yanzu haka Nadeem Anjarwalla, ba ya hannun Najeriya bayan da mahukuntan ƙasar suka tabbatar da cewa ya tsere, to amma wata majiya daga makusantansa ta ce ya bar Najeriya ne ta hanyar da ta dace.

Mahukuntan Najeriya dai sun ce suna aiki da jami’an tsaro don samar da takardar sammaci ga Mr Anjarwalla.

A ɓangare guda kuma, mahukuntan Najeriya sun maka kamfanin a gaban kotu inda suka shigar da tuhume-tuhume da suka shafi ƙin biyan haraji. In ji rahoton BBC.

tribune

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp