An haifa Harris ne a Oakland a jihar California. Mahaifiyarta ƴar asalin India ce, mahaifinta kuma ɗan asalin Jamaica ne.
Iyayenta sun rabu tana da shekara biyar, inda mahaifiyarta mai suna Shyamala Gopalan Harris ta ci gaba da kula da ita
Ms Harris ta taso ne tana cuɗanya da al’adun India, kasancewar tana yawan bin mahaifiyarta zuwa ƙasar. In ji BBC.
“Mahaifiyata ta san cewa ƴaƴanta biyu mata ne kuma baƙaƙe. Ta san cewa ƙasar da take zaune za su riƙa kallon ƴaƴanta a matsayin baƙaƙen fata ne, wanda hakan ya sa ta ƙuduri aniyar ƙarfafa mana gwiwa.”
Amma rayuwarta a jami’ar Howard, wadda ɗaya ce daga cikin manyan makarantu da baƙaƙen fata suke karatu ya sauya rayuwarta, inda ita ma ta ce zuwanta jami’ar ya matuƙar sauya mata rayuwa da tunani.