Taƙaddama ta ƙaure tsakanin gwamnatin APC mai barin gado da kuma ta jam’iyyar PDP mai zuwa a jihar Zamfara, bayan zargin cewa ƙananan kwamitocin karɓar mulki na gwamati mai jiran gado na wuce gona da iri.
Gwamnatin jihar ta yi zargin cewa ƙananan kwamitocin na zuwa ma’aikatun gwamnati suna yin bincike tare da karɓar bayanai, wanda a cewar ta abu ne da bai dace ba kuma ya saɓa wa Kundin Tsarin Mulki.
Gwamnatin APCn ta ce abubuwan da kwamitocin ke yi yi tamkar ‘kafa gwamnati ne a cikin wata gwamnati’, inda ta buƙaci da su jira har sai an miƙa musu mulki.
Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Ibrahim Dosara, ya shaida wa BBC cewa ƙananan kwamitocin sun kasance suna bin ma’aikatu suna karɓar bayanai da gudanar da bincike tare da karɓar bayanan asussan ajiya na ma’aikatun domin yin bincike.
“Duk bayanai da ake buƙata, ma’aikatun sun tattara tare kuma da miƙa wa kwamitin bayar da mulki, inda za su bai wa gwamna mai ci wanda shi kuma zai kira gwamna mai shigowa su zauna inda zai miƙa masa bayanan,” in ji Dosara.