Babban wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Syria, ya yi gargadin matukar ana son lamura su daidaita a kasar, dole sai an kai wa Syria daukin gaggawa sakamakon yakin da ya daidaita kasar.
Geir Pedersen, ya shaida wa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya cewa ba a kare yakin ba, duk da cewa an hambarar da mulkin Bashar al-Assad.
Ya yi misali da tashin hankali na baya-bayan nan tsakanin mayakan Kurdawa da kungiyoyin da Turkiyya ke mara wa baya a arewa maso gabashin kasar.
Ya ce “ana samun tashe-tashen hankula cikin makonni biyun da suka gabata, kafin a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta wadda Turkiyya da Amurka suka jagoranta.
Yarjejeniyar ta kwanaki biyar ta kare, ina cike da damuwar abin da zai faru nan gaba,” in ji shi.