Tawagar kwallon kafar mata ta Najeriya Super Falcons, za ta fara gasar cin Kofin Duniya da karawa da kasar Canada.
Tawagar ta Super Falcons,na rukuni daya da Canada, da Jamhuriyar Ireland da kuma kasar Australiya
Ranar Asabar ne aka fitar da jadawalin a birnin Auckland na kasar New Zealand daya daga cikin kasashen da za su karbi bakuncin wasan.
Najeriya na neman fadada kokarinta a gasar, wacce ita ce kasar da tafi kowacce kasa a nahiyar Afirka halartar gasar, inda ta halarci gasar sau tara, kuma ba ta taɓa fashin halartar gasar ba tun lokacin da aka fara ta.
Sauran kasashen da za su wakilci nahiyar Afirka a gasar sun hadar da Afirka ta kudu, da Zambiya, da Morocco. Sai kuma kasashen Senegal da Kamaru wadanda za su iya samun gurbi a gasar idan suka yi nasara a wasan cike gurbi da za su buga.
Kasashe 32 ne dai za su fafata a gasar, inda aka raba su zuwa rukuni takwas.
Tawagar mata ta Amurka ce ke rike da kofin, wanda ta ci kofin sau huÉ—u kuma na uku a jere.


 

 
 