Super Falcons ta isa Praia ne a daren ranar Asabar, gabanin wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Afirka na mata na 2024 da Cape Verde.
An sanar da zuwan zakarun na Afirka sau tara a hannunsu na X.
Sanarwar ta ce “Mun sauka lafiya a Praia, Cape Verde a yammacin yau, gabanin wasanmu na biyu a ranar 5 ga Disamba,” in ji sanarwar.
Super Falcons za ta fafata da Cape Verdea a wasa na biyu na wasan neman gurbin shiga WAFCON na 2024 a Estadio Nacional de Capo Verde, Praia ranar Alhamis.
Najeriya ta samu nasara a karawar farko da ci 5-0 inda Uchenna Kanu da Esther Okoronwko suka zura kwallaye biyu kowanne.
Dan wasan gaba na Tenerife, Gift Monday ya ci daya kwallon.


