Tawagar Super Falcons ta Najeriya sun isa Abuja bayan da suka yi nasara a gasar cin kofin Afrika ta mata ta 2024.
‘Yan wasa da jami’an kungiyar sun isa filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da yammacin ranar Litinin.
Za su gudanar da faretin na lashe gasar cin kofin ne tare a wasu gundumomi a babban birnin tarayya.
Ana sa ran tawagar za ta bi ta titin filin jirgin sama, Junction Berger, Maitama da Kasuwar Wuse.
Shugaban kasa Bola Tinubu ne zai karbi bakwancin Super Falcons a fadar shugaban kasa da safiyar yau.
Najeriya ta lashe gasar ta WAFCON karo na 10 a daren Asabar bayan da ta doke Atlas Lionesses ta Morocco da ci 3-2.