Tawagar Super Falcons ta Najeriya ta fice daga kasar a daren Lahadi, domin gudanar da atisayen kwanaki 15 domin tunkarar gasar cin kofin duniya ta mata ta FIFA 2023.
Zakarun Afirka sau tara za su kasance a Melbourne kuma za su yi wasannin sada zumunta don daidaita dabarun tunkarar gasar shekaru hudu.
Super Falcons ta na rukunin B tare da Australia da Canada da kuma Jamhuriyar Ireland.
Wasan farko na Randy Waldrum na gasar shine da zakarun Olympics, Canada ranar 21 ga watan Yuli a Melbourne.
Wasannin rukuni biyu na gaba da ‘yan Afirka ta Yamma da Australia da Jamhuriyar Ireland za su yi a Brisbane.
Super Falcons sun halarci duk bugu na gasar cin kofin duniya ta mata ta FIFA tun 1991.
Sun kai wasan daf da na kusa da karshe a shekarar 1999 a kasar Amurka.