‘Yar wasan baya ta Super Falcons ta kasa, Ashleigh Plumptre, ta ce, kungiyar ta shirya tsaf domin tunkarar abokan karawarta a gasar gayyata ta kasashe hudu da ake yi a Morocco.
Za a hada da tsoffin zakarun Afirka a gasar mai taken “Cup Cup” ta masu masaukin baki Mexico, Colombia da Costa Rica.
Tawagar Randy Waldrum za ta kara da Mexico a wasansu na farko a Leon a daren Laraba (yau).
Matan Najeriya dai ba su yi nasara ba a wasanni biyar da suka buga, sai dai Plumptre, wanda ke buga wa kulob din Leicester City na Ingila wasa, ta ce, za su kawo karshen tseren bakarare.
Plumptre ta ce, “Muna shirye-shiryen kowane wasa da sanin cewa muna kokarin yin nasara kuma za mu yi gasa gwargwadon iyawarmu don ganin mun samu sakamako,” in ji Plumptre a wata gajeriyar hirar bidiyo da aka buga a shafin Super Falcons na Twitter.
“Na shirya kaina a hanya guda don kowane wasa kuma a shirye muke mu tafi.”
Gasar za ta kasance wani bangare na shirye-shiryen Super Falcons na gasar cin kofin duniya ta mata ta FIFA ta 2023 da Australia da New Zealand za su dauki nauyin shiryawa.