A ranar Litinin 4 ga watan Satumba ne za a bude sansanin Super Eagles na neman shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za su yi da Sao Tome and Principe a birnin Uyo.
Za a yi wasan ne a filin wasa na Godswill Akpabio International Stadium, Uyo, ranar Lahadi, 9 ga watan Satumba.
Ana sa ran babban kocin, Jose Peseiro, zai fitar da jerin sunayensa na wasan a wannan makon.
Super Eagles ta riga ta samu tikitin zuwa gasar AFCON ta 2023 daga rukunin A.
Sao Tome and Principe, wadanda ke matsayi na karshe a rukunin, ba su da damar tsallakewa zuwa gasar.
Kasashen yammacin Afirka sun yi kunnen doki daya da rashin nasara hudu a wasanni biyar.
Saliyo da Guinea-Bissau za su kara a daya wasan na rukuni.
Cote d’Ivoire za ta karbi bakuncin gasar AFCON ta 2024 daga ranar 13 ga Janairu zuwa 11 ga Fabrairu.


