Super Eagles za ta fafata ne da Jamhuriyar Benin a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta 2026 a filin wasa na musammani.
Hukumar kula da kwallon kafa ta Afrika, CAF, ta ce filayen wasa a Benin ba su da inganci kuma ba za su iya daukar nauyin wasannin kasa da kasa ba.
Rahotanni daga kasar Benin na cewa, kungiyar kwallon kafa ta kasar na tattaunawa da takwararta ta Ivory Coast domin buga wasan a daya daga cikin filayen wasan da suka yi amfani da su a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2023.
Za a buga wasannin neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya tsakanin 3 da 11 ga watan Yuni.
‘Yan Najeriya za su karbi bakuncin Bafana Bafana na Afirka ta Kudu kafin su kara da Squirrels.
Super Eagles dai ita ce ta uku a rukuninta na neman tikitin shiga gasar da maki biyu bayan wasanni biyu da ta yi, yayin da Benin da ke karkashin jagorancin tsohon kocin Najeriya Gernot Rohr ke da maki.
Rwanda, da Afirka ta Kudu, da Zimbabwe, da Lesotho su ne sauran kungiyoyi a wannan rukunin.