Super Eagles za ta kara da Algeria a wasan sada zumunta na kasa da kasa a ranar Juma’a 23 ga watan Satumba.
Wasan sada zumuncin a cewar bayanai a shafin yanar gizon hukumar kwallon kafar Algeria, za a yi wasan ne a filin wasa na Mohamed Hamlaoui dake Constantine.
Super Eagles da ke gida ta kasa samun tikitin shiga gasar cin kofin kasashen Afirka (CHAN) na shekarar 2023 da Algeria za ta karbi bakunci.
Kungiyar Salisu Yusuf ta yi rashin nasara da ci 5-4 a bugun fenareti a hannun abokan hamayyar Black Galaxies ta Ghana.
An tashi wasan share fage da ci 2-2 a jumulla.
Algeria za ta yi amfani da wasan sada zumunta ne a wani bangare na shirye-shiryenta na CHAN 2023.
Su ma ‘yan arewacin Afirka za su kara da Sudan a wani wasan sada zumunci a ranar Alhamis 29 ga watan Satumba.