Filin wasa na Godswil Akpabio na kasa da kasa ake Uyo, zai karbi bakuncin dukkan wasannin gida na Super Eagles a wasannin neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya na 2026.
Shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ne ya bayyana hakan a wata ziyara da ya kai wa gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno a Uyo.
A ranar Lahadi 10 ga Satumba, 2023 filin wasa mai cin mutane 30,000 Super Eagles za su buga wasan karshe na neman gurbin shiga gasar cin kofin Afrika na 2023.
Idan dai za a iya tunawa, wannan katafaren filin ya karbi bakuncin Super Eagles a wasannin share fagen shiga gasar cin kofin duniya ta 2018.
Za a buga zagaye biyu na farko na wasannin neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya na shekarar 2026 tsakanin 13 da 21 ga watan Nuwamba.
Super Eagles dai sun kasance a rukunin D tare da Afirka ta Kudu da Jamhuriyar Benin da Zimbabwe da Rwanda da kuma Lesotho.
Kasashen da suka yi nasara a rukunin za su tsallake zuwa gasar cin kofin duniya na 2026 da Amurka da Canada da Mexico za su karbi bakunci, yayin da wadanda suka zo na biyu za su buga wasan neman karin gurbi a Afirka.