Yanzu haka dai Super Eagles za ta je sansaninta ne a ranar Talata, 28 ga watan Mayu, domin karawa da Bafana Bafana ta Afrika ta Kudu wasan shiga gasar cin kofin duniya ta 2026.
Tun da farko dai an shirya ‘yan wasan za su isa sansanin ne a ranar Asabar 1 ga watan Yuni.
Yanzu haka kungiyar za ta hallara a Uyo kwanaki uku kafin fara shirye-shiryen tunkarar muhimmin wasan.
Tawagar Finidi George za ta kara da Bafana Bafana a filin wasa na Godswill Akpabio International Stadium, Uyo a ranar Juma’a, 7 ga watan Yuni.
Haka nan kuma za su fafata da ’yan kunar bakin wake na Benin kwanaki kadan bayan haka.
Super Eagles dai tana matsayi na uku a rukunin C da maki biyu a wasanni biyu.
Rwanda ce ta daya a rukunin da maki hudu, yayin da Afirka ta Kudu ke matsayi na biyu da maki uku.