Kungiyar Super Eagles ta Najeriya ta ci gaba da zama a matsayi na 39 a jadawalin hukumar FIFA na wata-wata da ta fitar ranar Alhamis.
Haka kuma kungiyar Jose Peseiro ta ci gaba da rike matsayin ta na shida mafi kyau a Afirka.
Super Eagles dai na bayan Morocco, Senegal, Tunisia, Algeria da Masar a nahiyar.
A watan Yuni ne ‘yan wasan Afirka ta Yamma suka yi nasara a kan kungiyar kwallon kafa ta Leone Stars ta Saliyo da ci 3-2 a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin Afirka na 2023 a Monrovia.
Zakarun Afirka sau uku a gaba za su kara da Sao Tome and Principe a wasan neman gurbin shiga gasar AFCON ta 2023 a watan Satumba.
Babu wasu canje-canje kwata-kwata a cikin manyan kasashe goma, wadanda suka kunshi kungiyoyin Turai da Kudancin Amurka kadai.
Zakarun duniya Argentina ne ke rike da matsayi na daya a jerin kasashen.
Za a buga matsayi na gaba a ranar 21 ga Satumba.