A ranar Juma’a ne dai Super Eagles din suka yi jinkiri na wasu sa’o’i a Abidjan sakamakon sauya tsarin tafiyarsu zuwa Uyo.
Kungiyar Augustine Eguavoen ta fafata da Jamhuriyar Benin a filin wasa na Felix Houphet Boigny, Abidjan a daren ranar Alhamis.
Zakarun na Afirka sau uku sun rike mai masaukin baki da ci 1-1.
Tun da farko dai ana sa ran tawagar za ta bar Abidjan da karfe tara na safe agogon kasar.
Ana sa ran za su fara sauka a Legas kafin su yi hanyar Uyo.
‘Yan wasan za su tsallake atisaye a yau.
Super Eagles za ta kara da Rwanda a filin wasa na Godswill Akpabio International Stadium, Uyo ranar Litinin mai zuwa.