Kungiyar Super Eagles ta Najeriya ta yi watsi da matsayi biyar a jadawalin da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta fitar.
Super Eagles yanzu ita ce ta 40 mafi kyau a cikin jadawalin watan Afrilu da FIFA ta fitar a ranar Alhamis.
Ku tuna cewa Najeriya ita ce ta 31 a jerin gwanaye a duniya a jadawalin watan Disamba.
Sai dai a halin yanzu kungiyar Jose Peseiro ita ce ta 6 mafi kyau a nahiyar Afirka, yayin da Morocco ke matsayi na daya a Afirka kuma a yanzu ita ce ta 11 mafi kyau a duniya.
Bayan Morocco akwai Senegal, Tunisia, Algeria, Masar da Najeriya.
Sai dai kuma Argentina ce ta daya a duniya, sai Faransa da Brazil da Belgium da Ingila da Netherland da Croatia da Italiya da Portugal da kuma Spain a matsayi na 10.
Sauran wadanda suka yi jerin sunayen daga 11-20 sun hada da Morocco, Switzerland, Amurka, Jamus, Mexico, Uruguay, Colombia, Senegal, Denmark da Japan.