Dan wasan gaba na kungiyar Super Eagles, Victor Osimhen ya ce dole ne kungiyar ta tunkari wasanta na gaba da Guinea-Bissau a gasar cin kofin Afrika na 2023 da muradin samun nasara.
Osimhen ya dage cewa yana da kyau Super Eagles kada su raina mutanen Baciro Cande.
“Muna da burin samun kwarin guiwa a karawar da Guinea-Bissau. Babu shakka za su tunkari wasan da azama, kuma ba za mu raina kowace kungiya ba, idan aka yi la’akari da abin da suka yi na samun cancantar,” in ji Osimhen bayan wasan.
“Mun hadu da su a wasannin share fage kuma mun san karfinsu. Sun ci mu a gida, yayin da mu ma muka doke su.
“Don haka, muna sa ran za a yi wasa mai tsauri da su. Za mu yi iya kokarinmu don samun nasara.”
Super Eagles ta koma matsayi na biyu a rukunin A bayan da ta doke Cote d’Ivoire da ci 1-0 a ranar Alhamis.
Tawagar Jose Peseiro tana bukatar canjaras ne kawai daga wasan da suka yi da Guinea-Bissau domin samun gurbin zuwa zagaye na 16.
Za a yi karawar ne a filin wasa na Felix Houphouet Boigny da ke Abidjan ranar Litinin mai zuwa.


