fidelitybank

Sunusi na da alaka mai kyau da Tinubu – Fadar Shugaban Kasa

Date:

Fadar shugaban kasa ta mayar da martani game da iƙirari shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano cewa shi ne ke goyon bayan Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero a rikicin masarautar jihar da ake yi tsakaninsa da Muhammadu Sanusi II.

Ɗaya daga cikin masu taimaka wa Shugaba Tinubu kan yaɗa labarai, Abdu’aziz Abdul’aziz ya ce Shugaban Ƙasa Tinubu na da alaƙa mai kyau da duka ɓangarorin biyu “musamman ma Muhammadu Sanusi II”.

Ya ƙara da cewa maganar zargi ne kawai “maras tushe”.

“Abin da mai maganar bai sani ba ko kuma bai faɗa ba saboda siyasa shi ne; shugaban ƙasa na da alaƙa mai kyau da duka waɗanda ke taƙaddama a kan wannan sarauta,” in ji shi.

“Musamman ma Sarki Sanusi II, wanda suke da alaƙa tun lokacin da ya nemi sarautar a 2014. Kuma ya sani cewa Sarki Aminu Ado bai taɓa zuwa ya ga Bola Tinubu a fadar shugaban ƙasa ba tun lokacin da ya hau mulki.

“Amma Sanusi II ya zo ba sau ɗaya ba kuma ya ga shugaban ƙasa. Wannan ya nuna irin alaƙar da ke tsakaninsu. Wani mutum ya fito yana magana a kan wani abu da ba shi da hujja abin takaici ne.”

network news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp