Firaministan Birtaniya Rishi Sunak ya gana da shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas, yayin ziyara da ya kai Masar a yau Juma’a.
Ofishin Sunak ya ce Firaministan ya miƙa ta’aziyyarsa ga waɗanda suka rasa ƴan uwansu a Gaza, inda ya nanata buƙatar ganin an buɗe hanyar kai kayan agaji zuwa Gaza.
Dukka shugabannin sun yi Alla-wadai da harin Hamas, inda suka ce Hamas ba ta wakiltar al’ummar Falasɗinawa.
Mai magana da yawun Sunak ya ce: “shugabannin sun amince cewa dukka ɓangarorin su ɗauki matakan kare fararen hula da kuma gine-ginensu, da guje wa asarar rayuka


