A yayin da ake ci gaba da takun-saka da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike da Gwamna Sim Fubara na Jihar Ribas, a yanzu haka gwamnan ya ce matakin da ya dauka na rungumar yarjejeniyar zaman lafiya da Shugaba Bola Tinubu ya kulla a tsakanin su, ba wai tsoro ba ne gudun magana ne kawai.
Fubara ya ce ya dauki matakin ne domin ganin an samu zaman lafiya a jihar.
Ya yi wannan jawabi ne a wajen liyafar da gwamnatinsa ta gudanar a gidan gwamnati da ke Fatakwal, kamar yadda wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Boniface Onyedi ya fitar.
Fubara ya ce gwamnatinsa ba za ta tsunduma cikin duk wani kazamin yakin siyasa da zai kawo cikas ga alkiblar ci gaba a jihar ba.
Ya ce, duk yarjejniyar da suka kulla ba don tsoro ba ne, amma saboda suna da muradin mutanen jihar, kuma suna girmama dattawa.
Fubara da Wike sun yi takun-saka kan tsarin siyasa a jihar Ribas.
Rikicin dai ya sa wasu ‘yan majalisar dokokin jihar suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, yayin da wasu kwamishinonin suka yi murabus.
Sai dai an soki Fubara da rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar saboda wasu sharuddan da ake zargin ba su amince da shi ba.


