fidelitybank

Sulhu da ‘Yan Bindiga shi ne mafita – Tsohon Gwamna

Date:

Tsohon gwamman Zamfara Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura ya ce zama teburin sulhu da yan bindiga ne hanyar da ta fi dacewa na kawo ƙarshen matsalar tsaron da ta addabi yankin arewa maso yammacin Najeriya.

A cewarsa, irin zama teburin sulhu da gwamnatin tarayya ta yi da yan Neja Delta a kudancin Najeriya, idan aka bi irin tsarin, za a iya shawo kan matsalar tsaron a yankin arewa maso yammaci.

Ya ce yana kira ga sabbin manyan hafsashin tsaro da su zauna da ‘yan bindigar kamar yadda a baya aka zauna da ‘yan bindigar da suka addabi yankin Naija Delta a fara maganar sulhu da su.

”Ai ‘Yan Najeriya ne yawancinsu, an ce akwai mutanen waje, amma su ‘yan Najeriya ɗin a zauna da su a jawo hankalinsu a nuna musu yadda aka yi wa ‘yan Naija Delta, yadda aka sakar musu kudi bayan yin sulhun da su aka sakar musu kudi, suka fara sana’o’i da abin yi, su ma waɗanan nan a zauna da su a samar musu hanyar cin abinci”.

Yariman Bakuran ya ce idan hakan ta gagara to sai a bi su duk inda suke a ɗauki matakin da ya dace.

Dangane da sulhu da ‘yan bindigar, da wasu jihohin ƙasar suka yi yunƙurin yi a baya, wanda kuma bai yi nasara ba, Yariman Bakura ya ce ba a yi sulhun na gaskiya ba.

Sanata Yarima ya ce ”ba wai zama da su a yi musu alƙawari, sannan a watse ne sulhu ba, ni na bibiyi duk sulhun da aka yi da su a bayan, duka alƙawuran da aka yi musu an saɓa, domin ba za ka kira mutumin da talauci da jahilci suka sanya shi shiga daji sannan ka yi tunanin yin sulhu da shi ba tare da cika masa alƙawuran da ka ɗauka masa ba”.

A filinmu na Gane mini Hanya na wannan makon Awwal Ahmad Janyau ya tattauna da tsohon gwamnan na Zamfara kan batutuwa da dama inda ya soma tsokaci kan yadda yake kallon kamun ludayin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

latest news in nigeria today 2022

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp