Gwamnatin jihar Borno ta sanar da cewa za ta rage wa manoman da suka sha fama da hare-haren Boko Haram kuɗin mai domin rage musu raɗaɗi.
Gwamna Babagana Umara Zulum ne ya sanar da haka a ranar Juma’a a garin Bama yayin rabon tallafin kayan aikin gona ga manoma sama da 5,000 waɗanda hare-haren Boko Haram ya ɗaiɗaita.
A cewar gwamnan, za a rage kuɗin litar mai wanda ake sayarwa kan naira 1,000 da kuma 1,200 a Maiduguri zuwa 600 ga manoman.
“Mun yi haka ne da zimmar rage wa manoman raɗaɗi ko kuma matsalolin kuɗi da suke fuskanta, musamman ma a yankuna da aka lalata wa gine-gine da kuma wuraren kasuwanci sakamakon rikicin Boko Haram na tsawon shekaru,” in ji Zulum.
BornoAsalin hoton,Gwamnatin Borno
Gwamnan ya ce sun yi irin wannan hoɓɓasa a kananan hukumomin Damasak da Mobar a shekara da ta wuce, inda hakan ya sa aka samu ƙaruwar abinci da ake noma wa da kuma kyautata rayuwar mutane.
Ya ce za su yi aiki da sojoji wajen tabbatar da cewa an kai man fetur ɗin ba tare da wata matsala ba.
Cikin kayan da gwamnan ya raba sun haɗa da buhunan taki kirar NPK guda 2000 da kuma injunan tuka-tuka 1000.